ABNA24 : Da yake sanar da hakan, babban mai gabatar da kara na gwamnatin Madagaska, ya ce, ana tsare da faransawa tun ranar Talata.
A cewarsa, masu bincike a kasar na da kwararen hujjoji na cewa mutanen biyu na shirya kashe wasu manyan jami’an kasar ciki har da shugaba Andry Rajoelina.
Lauyoyin mutanen biyu dai basu samu ganawa dasu ba.
Bayanai sun ce an cafke Paul Rafanoharana a gidansa ranar Talata, yayin da shi kuwa Philippe François, aka cafke shi a filin jirgin Ivato, yayin da yake shirin barin kasar zuwa Faransa.
342/